• Labaran yau


  Yadda uwargida ta guntule mazakutar Mijinta yana tsakar bacci

  Lamarin ya farune a garin Tella dake karamar Hukumar Gassol dake jihar Taraba inda Aliyu Umar yana bacci matarsa, Halima ta dauko wuka ta yanke masa Al’aura.

  Lamarin ya faru a jiya, Talata inda dan uwan Aliyu yace sun garzaya dashi Asibiti kuma an bashi kulawar data kamata, saidai yace sun canja masa asibiti zuwa na jihar Gombe dan bashi kulawa ta musamman.Yace ‘yan uwa sun so su kashe matar me ciki amma aka tseratar da ita.

  Me magana da yawun ‘Yansandan jihar,DSP  David Misal ya tabbatar da faruwar lamarin ga Dailytrust inda yace an kama wadda ake zargi kuma ana kan bincike.

  hutudole


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda uwargida ta guntule mazakutar Mijinta yana tsakar bacci Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama