Wani É—an achaba a kasar Uganda ya mutu bayan ya cinna wa kansa wuta da
nufin nuna fushinsa, bayan `yan sanda sun ƙi ba shi babur ɗinsa da suka
kama.
‘Yan sanda sun ce dan achaban, mai suna Husseini Walugembe ya bai
wa abokinsa ne É—anin babur É—in, kuma sai aka yi rashin sa`a `yan sanda
suka kama shi da goyon fasinja, alhali an haramta yin haka ƙarƙashin
dokokin yaƙi da cutar korona.
An ce takaici ne ya kama dan acaban bayan ya yi ta zuwa ofishin `yan sanda domin su ba shi babur din nasa, amma suka ƙi.Da
ya ga abin ya gagara, sai ya shiga cikin wani daki a harabar ofishin
`yan sandan, kana ya kulle ya yayyafa wa jikinsa man fetur din da ya
É—ura a cikin wata kwalbar ruwa, sannan ya cinna wa kansa wuta.
Yan sanda
dai sun ce suna gudanar da bincike a kan zargin da ake yi cewa jami`ansu
na karɓar cin hanci kafin su saki baburan da suka kama.
Hutudole
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari