Wata Sabuwa:Ma’aikaciyar dake karkashin Minista Akpabio tace ta taba fallamai mari saboda cin zarafinta

Rahotun hutudole
Badakalar cin Biliyoyin Nairori a ma’aikatar Nija Delta ta NDDC karkashin Ministan wannan ma’aikata, Godswill Akpabio na ci gaba da yamutsewa.
A baya mun kawo muku yanda tsohuwar Dirakta a ma’aikatar Joi Nuneih take bayyana yanda Akpabio yaso ya tirsasa mata ta taimaka mai ya ci kudi, inda har wani me kare mura dunshi yaso hanata ganawa da manema labarai.
Daga baya Akpabio yace matar tana da matsala dan aurenta 4 kenan kuma a tambayi tsaffin mazanta irin halinta aji.
Saidai a yau ta zo da wata sabuwar zargi inda ta bayyana a hirar da Arise TV ta yi da ita cewa ta taba marin Ministan saboda yaso cin zarafinta.

Majalisar tarayya dai tace ba zata bari badakalar kudin NDDC ta tafi hakanan ba ba tare da ta bincike ta ba.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post