Tsohon shugaban kasar Sudan Al-Bashir ya gurfana a Kotu sakamakon jiyin mulkin 1989

Tsohon shugaban kasar Suda Omar Al-Bashir wanda ya dare Karagar mulki bayan wani juyin mulki na soji a shekarar ,ya gurfana a gaban Kotu sakamakon juyin mulkin.

Dan shekara 76,  Al-Bashir ya gurfana a gaban Kotu tare da fiye da mutum 20 manyan jami'an Gwamnatinsa ciki har da mataimakinsa Ali Osman Taha, da Bakri Hassan Saleh.  Adadin ya hada da fararen hula da manyan jami'an soji da ya mulki kasar tare da su.

Ana zargin Al-Bashir da keta dokokin aikin soji tare da aikata ba daidai ba a lokacin mulkinsa.

Ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 1989, Janar Umar Al-Bashir ya jagoranci wasu sojoji suka kifar da Gwamnatin shugaban kasar Sudan na farar hula a wancan zamani shugaba Sadiq Al-Mahdi, daga wannan lokaci Al-Bashir ya mulki kasar Sudan har fiye da shekara 30.

Al-Bashir zai iya fuskantar hukuncin kisa idan Kotu ta same shi da laifi.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post