Tanzu yanzu: Gwamnan Plateau ta haramta Sallar Idi saboda korona

Gwamnatin Jihar Plateau ta haramta Sallar Idi a jihar a bana yayin da adadin mutanen da suka kamu da cutar a jihar ta kai 982. Shugaban kwamitin yaki da COVID-19 na jihar, Gwamna Simon Lalong ne ya sanar da haramcin yayin jawabin da ya yi wa manema labarai kan matakan da jihar ke dauka kan annobar a ranar Talata a Jos.

Gwamnan ya kuma haramta duk wasu bukukuwa da aka saba yi da sallah da suka hada da ziyartar wuraren shakatawa da gidajen dabobin namun daji da sauransu. "Dukkan mazauna jihar suyi amfani da takunkumin fuska, musamman yara a lokacin da suke kai wa yan uwa da abokan arziki abinci," in ji shi.

Mr Lalong ya ce hakan ya zama dole ne bayan karuwar adadin masu cutar da aka samu a jihar tare da bikin sallar da ke karatawo domin dakile yaduwar cutar.

Gwamnatin tarayya dai ta sanar da ranakun Alhamis da Jumaa a matsayin ranakun hutu domin musulmi su yi bikin sallar babba. Gwamnan wanda ya samu sakataren gwamnatin jihar, Danladi Atu, ya wakilta ya shawarci dattawa su zauna a gida duba da cewa suna suka fi rauni idan cuta ta kama su.

Mr Lalong ya kuma tunatar da mazauna jihar game da dokar takaita fita da gwamnatin tarayya ta saka na karfe 4 na asuba zuwa 10 na dare tana nan tana aiki.

Ya ce an samu karuwar mutanen da suka kamu da cutar a jihar saboda akwai dakin gwaje gwaje guda uku a jihar: Cibiyar Binciken Dabobbi ta Kasa da ke Vom; Asibitin Kwararru da ke Plateau da Asibitin Koyarwa ta Jamiar Plateau.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN