A baya dai kakakin majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawal ya karyata cewa an basu wani kaso na daukar aikin N-Power..
Saidai
shugaban kwamitin dake kula da bangaren rage radadi Talauci na
majalisar Wakilai, Abdullahi Balarabe Salaame ya bayyana cewa an ware
musu wani kaso na aikin N-Power.
Yace an baiwa ‘yan Majalisar wani kaso
na aikinne saboda yanda a baya suka ga yanda ake kashin dankali wajan
samun aikin yanda zaka ga wani bangarene kawai na kasarnan ke amfana da
abin.Yace ba duka guraben aikin aka basu ba, wani kaso ne daga ciki.
Ya
bayyana hakane a hirar da yayi da BBC. Da aka tambayeshi ko ba zasu yi
amfani da wannan dama wajan cimma manufofinsu na siyasa ba? Sai yace ai
shima shugaba Buhari da ya fito da tsarin Manufofin siyasarsane yake
cimmawa dashi.
Yace sun wa mutane alkawurra lokacin da suke kamfe dan
haka wannan abu na daya daga cikin amfanuwar da zasuwa mutanensu.
Hutudole
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari