Matashi ya nuna wa dan Majalisar tarayya mai wakiltar Zuru yatsa kan hanya mai bullewa

Yayin da yake ci gaba da more kujerar wakilcin jama'ar da yake wakilta a Masarautar Zuru a  Majalisar wakilai na tarayya, wani matashi dan kasar Zuru ya shawarci Dan Majalisan tarayya Hon. Kabiru Tukura kan ya gyara sirdinsa domin zamansa ya dore daram yayin da ake ci gaba da tafiyar wakilcin siyasa da yake yi wa al'ummansa.

Matashi Hisham Suleman ya ce " Allah yabaka dama Amma kanason kayi watsi da ita HON inada tabbacin cikin kowani wata kana kashin kudi hiyega million 5 mafi yawan kudin kanaba yansiyasane , HON mafi yawan mutanen zuru sunzabekane don sunada yakini cewa zasu samu canji daga mulkinka amatsayinka na matashi


Amma sai gashi hakarsu Bata cimma ruwaba shawarata gareka HON idai har kana iya kashe kudi har million 5 kowani wata mizaihana kataimaki mutanen kasar ZURU EMiRATE dasu ta hanyar yimusu kujerun makaranta, saboda kowata million 5 tana kera kujera 1000 kaga ashekara kanada kujeru 12,000, kokuma keke Dunki suna sayen 300 ashekara,ko injimin banruwa suna sayen 550, da dai sauransu ".

Tuni dai kalaman Hisham suka ja hankalin matasan kasar Zuru wanda hakan ya ankarar da su kan alkiblar siyasar Hon Kabiru Tukura wanda ya sami karbuwa da gagarumar rinjaye a siyasar 2015 da kurar "sai Baba Buhari" ya kwasa musamman a Arewacin Najeriya.

Hon Kabiru ya kasance manuni ga zarran matasa bisa tsammani da manufa, kasancewa shi kansa matashi ne da matasan kasar Zuru ke wa kallon wanda zai iya kai matasa tudun tsira a siyasance, da kuma fuskantar matsaloli da kalubalen da matasan Zuru ke fuskanta da zimman rage radadin da suke fama na rashin katabus balle nasssara a tsarance ga kalubalensu.

Sai dai wani matashi dan Masarautar Zuru da baya son a ambaci sunansa, ya shaida mana cewa " Gaskiya ina ganin da wuya Hon Tukura ya karbi shawaran wannan matshi idan ka yi la'akari da tsarin siyasar abin da ake zargin cewa tsari ne na uwayen gidansa a siyasance. 


Domin hanyar da yake bi a yanzu a siyasance ba hanya bace mai bullewa a nawa ra'ayi. Domin dole ne Kabiru ya fuskanci gaskiya kuma ya yi aiki kamar matashi ba tsari da muka sani kaka da kakanni ba a siyasan Zuru kuma shi da kansa ya dinga maimaitawa. A matsayinsa na matashi, muna bukatar gani sabon tsari wajen tafiyar da harkokinsa na siyasa a kasar Zuru".


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN