Sau uku ƙarti uku suna danne ni ana sake karya ni a ɗorin gida

Ɗorin gargajiya ko ɗorin gida hanya ce da aka daɗe ana amfani da ita wajen gyaran karaya shekaru aru-aru kuma sanannen abu ne cewa ana iya ɗorin gida a dace har a warke sumul.

Sai dai abu mai matuƙar muhimmanci da ya kamata a gane shi ne ba kowace irin karaya ce ake yin ɗorin gida kuma a wanye lafiya ba. Domin karayar ƙashi iri-iri ce, wata sassauƙar karaya ce, wato ƙashin ya ƙarye biyu ne kawai kuma bai fasa fata ya fito waje ba, wata kuma ƙashin yana kakkaryewa ne rugu-rugu.

Saboda haka, sanin haƙiƙanin wacce irin karaya ce ta faru sai an ɗauki hoton wurin sannan a gane, amma ba da gani da ido kawai ba ko kuma shafawa ko lalume da hannu. Bayan an tabbatar da wacce irin karaya ce, sannan likitan tiyatar ƙashi ya zaɓi hanyar ɗori da za ta dace da karayar.

Amma abun takaici ne da kuma rashin sanin ƙima da haƙƙin ɗan Adam yadda kasuwar ɗorin gida take ci barkatai ba tsari. Sau da yawa sai ka ga an kawo mutum asibiti da ɗorin gida bayan hannu ko ƙafa ta lalace, wani lokacin ma sai dai a yanke.

Abu ne da muka saba ji a cikin al'ummarmu, ka ji mai ɗorin gida ya ce wai karayar ba ta ɗoru ba, musamman ma idan ba shi ne yai ɗorin tun da farko ba. Saboda haka sai an gayyato ƙarti sun riƙe mutum an sake karya shi domin sake ɗorin.

Wannan baƙar azaba ce da waɗanda suka karye kuma suka tsinci kansu a hannun masu ɗorin gida suke sha babu gaira babu dalili!

Wata da ta karye a cinya ta ba da labarin yadda aka riƙa tara ƙarti uku suna riƙe ta ana karya ta har sau uku. Saboda a duk lokacin da aka ɗora ta kuma ƙafar ta ƙi warkewa sai a sake gayyato wani mai ɗorin, shi kuma sai ya ce ai daman ba ta doru ba, saboda haka sai an sake karya ta an sake ɗorin.

Haka akai ta yi har sau uku, amma duk ɗorin bai yiwu ba, saboda masu ɗorin ba su san haƙiƙanin irin karayar da ta faru ba.

Daga ƙarshe dai aka tattatara aka taho asibiti don neman ɗaukin likita bayan masu ɗorin gida sun lashe maƙudan kuɗaɗe baya ga irin lahanin da suka haifar a ƙafar.
Allah ya kyauta, ya kuma sa mu gane.

Physio Hausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN