• Labaran yau


  Sabina yar Zuru da Rueben sun Musulunta a babban Masallacin Juma'a na jihar Kebbi

  Wasu bayin Allah guda biyu, na miji da mace, sun karbi addinin Musulunci a babban Masallacin Juma'a na jihar Kebbi (Central Mosque) a garin Birnin kebbi bayan Sallar Juma'a ranar 17 ga watan Juli 2020.

  Sabina ta zama Zainab
  Wadanda suka Musulunta sune Malama Sebina 'yar asalin kasar Zuru a kudancin jihar Kebbi, wacce ke tare da kananan yaranta guda uku ta canja sunanta zuwa Zainab, da Mr Rueben dan asalin garin Port Harcourt wanda ke karatu a Kwalejin koyon fasaha ta Umaru Waziri a garin Birnin kebbi, ya canja sunansa zuwa Usman.
  Rueben ya zama Usman

  Limamin Masallacin Imam Muhktar Abdullahi (Walin Gwandu) ne ya jagoranci Kalaman shahada kuma Zainab da Usman suka amshi Kalman shahada suka zama Musulmi nan take.
  Zainab da 'ya'yanta uku


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Sabina yar Zuru da Rueben sun Musulunta a babban Masallacin Juma'a na jihar Kebbi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama