Na hannun damar Buhari, Ismail Funtua, ya rasu

Mallam Ismaila Isa Funtua, makusancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rasu a daren yau, Litinin, 20 ga watan Yuli.

Mariga Funtua ne manajan darektan kamfanin jaridar 'Democrat' na farko, sannan ya taba rike shugaban kungiyar masu kamfanin jarida a Najeriya (NPAN).

Jaridar 'ThisDay' ta rawaito cewa Funtua ya mutu ne sakamakon ciwon zuciya. Har ya zuwa mutuwarsa, marigayi Funtua na daga cikin dattijai a kungiyar NPAN, sannan shine shugaban

kamfanin gine - gine mai suna 'Bulet Construction Company'.

Za a yi jana'izarsa da safiyar ranar Talata bisa tsarin addinin Musulunci.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN