Matsalar rubutu bayan shanyewar ɓarin jiki da abin da ya kamata a yi

Physio Hausa


Daga cikin ƙalubalen da masu fama da shanyewar ɓarin jiki ke fuskanta akwai kasa rubutu ko kuma walkacewar rubutun. Sau da yawa mai fama da shanyewar ɓarin jiki kan gaza rubuta sunansa, sa hannu a takarda ko kuma zane.

Wannan matsala ta rubutu na faruwa sakamakon raunin / riƙewar hannu, rashin dai-daito da saiti waɗanda ke haifar da rawar hannu ko walkacewar rubutu ko zane.
 
Har wa yau, wannan matsala ta fi kawo cikas ga malaman makaranta, ɗalibai, ma'aikatan ofis, masu sana'ar zane ko fenti da sauransu, musamman idan hannun da mutum ke rubutu da shi ne ya shanye. Hakan kuma na kawo barazana ga sadarwa, koyo da koyarwa, da kuma sirrin mutum.
 
A yayin da hannun mai shanyewar ɓarin jiki ya kai matakin iya rubutu kuma aiki ko sana'arsa na buƙatar rubutu, likitan fisiyo zai tsara masa tsarin sake koyon rubutu cikin sauƙi har rubutunsa ya iya karantuwa.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari



أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN