Masu sace mutane 2 sun yi mutuwan gaggawa an kama 2 masu basu labaran sirri

An kashe masu satar mutane domin karban kudin fansa guda biyu, kuma aka kama masu basu labaran sirri su biyu a kan babban hanyar Lokoja zuwa Okene bayan yan sa kai na karamar hukumar Okehi da Adayi sun farmake su a maboyarsu.

Rahotanni sun ce wadannan masu sace mutane sun dade suna addaban jama'a a wannan hanyar kafin dubunsu ta cika.

Babban mai ba da shawara kan harkar tsaro na karamar hukumar Okehi,  Hon Abdulraheem Ohiare tare da takwaransa na karamar hukumar Adavi , Hon Joseph Omuya Salami sun jagoranci mafarauta suka je maboyan wadannan bata gari bayan sun sami labarin sirri kuma suka kashe bata garin bayan musanyar harbin bindigogi.

Daga bisani mafarautan sun kama wani Mr Godwin Peter dan garin Ikeje a karamar hukumar Olamaboro mai ba da labaran sirri ga masu satan mutanen tare da takwaransa Sanni Habib dan garin Idoji a karamar hukumar Okene.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post