Majalisar dattawa ta samar da sabuwar dokar daurin rai-da-rai ga masu garkuwa da mutane

Rahotun Legit

Majalisar dattawan tarayya a ranar Talata, 14 ga watan Yuli ta samar da sabuwar dokar daurin rai-da-rai ga duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a Najeriya, The Punch ta ruwaito.

Majalisar ta yanke shawarar canza dokar ne daga daurin shekaru 10 a gida gyara hali zuwa daurin rai-da-rai Dokar wacce Sanata Oluremi Tinubu, ta shigar na da take "Bukatar canza dokar laifi CAP. C.38 na dokokin tarayyar Najeriya 2004.

" Hakazalika, dokar ta canza tsarin cewa wajibi duk wacce aka yiwa fyade ta kai kara cikin wani takaitaccen lokaci na watanni biyu, ko a karyata ta. Bayan haka, an sauya tsarin cewa mata kadai ake yiwa fyade, yanzu dokar ta hada da maza.

A yanzu, komin dadewa da yiwa mutum fyade, zai iya shigar da kara kuma a saurara. Yanzu za'a tura dokar majalisar wakilai domin su amince d dokar kafin kaiwa shugaban kasa ya rattafa hannu.

Laifukan garkuwa da mutane da fyade sun zama ruwan dare a cikin al'ummar Najeriya, daga kudu zuwa Arewa, babu inda ba'ayi. Fari da laifin garkuwa, an sace daruruwan mutane a hanyoyin Najeriya, a gidajensu, a gonakinsu, a wuraren aikinsu, da sauran su.

Sabanin yadda aka saba a baya na sace masu hannu da shuni, yanzu abin ya game kowa har talaka bawan Allah bai tsira ba. Hanyoyin da garkuwa da mutane ya fi yawaita a Najeriya sun hada da hanyar Abuja zuwa Kaduna, Kaduna zuwa Zariya, Abuja zuwa Lokoja, Kaduna zuwa Birnin Gwari, Lokoja zuwa Okene, dss.

Kawo yanzu an damke daruruwan matasan da ke aikata wannan aika-aika kuma suna gurfana a kotu. Daga cikinsu akwai manya irinsu Evans, da Hamisu Wadume. Hakazalika laifin fyade ya zama ruwan dare musamman zakkewa kananan yara maza da mata.

Cikin yan kwanakin nan, an samu mahaifi ya yiwa diyar cikinsa fyade, kato ya zakkewa jaririya, da yiwa luwadi da kananan yana musamman Almajirai.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN