Lamari ya lalace: An kama ɗan babban Limami da laifin yi wa 'yar shekara 12 fyaɗe

Yaron wani Fasto da wasu mutane biyar da ake zargi da aikata fyade, a yanzu haka an garkame su a dakin ajiye masu laifi na ofishin rundunar 'yan sandan jihar Akwa Ibom da ke birnin Uyo.
Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, CSP N-Nudam Fredrick, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a karshen mako.
Ya ce duk mutane shidan da ake zargi sun amsa laifin biyan bukatarsu ta sha'awa da budurwa matashiya mai kananan shekaru.
A rahoton da jaridar Vanguard ta ruwaito, ababen zargin sun shiga hannu ne bayan an shigar da korafi ga ofishin 'yan sandan kan ta'asar da suka aikata.
A cewar CSP Fredrick, kwamishinan 'yan sanda na jihar Edgar Imohimi, ya lashi takobin cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kwato hakkin matan da aka ketawa haddi.

Ya nakalto kwamishinan 'yan sandan yana shawartar duk wadanda suka fada tarkon fyade a kan kada su ji tsoro ko kunyar shigar da kara domin a nema musu hakki.
CP Imohimi ya kuma yabawa hukumar shari'a ta jihar dangane da yadda ta ke gaggauta zartar da hukuncin kan miyagun mutane masu ta'adar fyade.
Ya kara da cewa, irin wannan mugun hali ba za su taba samun wani sukuni ko wata nutsuwa ba matukar sun shiga hannu.
Wani rahoto mai nasaba da wannan da Legit.ng ta ruwaito, rundunar ‘yan sandan Najeriya sun wanke shararren Mawakin nan wanda aka sani da D’Banj daga zargin da wata Seyitan Babatayo ta yi masa na yi mata fyade.
A wani jawabi da ‘yan sanda su ka fitar ta bakin DCP Umar Sanda a madadin mataimakin sufeta janar na kasa wanda ke lura da binciken laifuffuka, an yi fatali da wannan zargi.
Kamfanin dilllacin labarai na kasa, NAN ya ruwaito cewa, ofishin FCID na ‘yan sandan ya na cewa babu hujjar da ke nuna Tauraron ya yi lalata da Seyitan Babatayo da karfin tsiya.
Sanarwar ta bayyana cewa, Miss Seyitan Babatayo ta jefi D’Banj da zargin yi ma ta fyade da kokarin yi wa maganar rufa-rufa.
Ko da cewa Seyitan ta yi wasa a wannan otel, jami’an ‘yan sanda sun ce babu abin da zai nuna Oladapo Daniel Oyebanjo ya yi lalata da ita, don haka aka kashe maganar.
DCP Sanda ya ce bincike ya nuna babu gaskiya a korafin da Seyitan Babatayo ta yi na cewa Oladapo Daniel Oyebanjo watau D’Banj ya yi amfani da ita ba tare da iznin ta ba.
Source: Legit

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post