Kyautar raguna na bayar kuma wanda na ga dama zan ba kyauta na a Zuru - Inji Yombe

Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alhaji Samaila Yombe Dabai ya bayyana ra'ayinsa kan kyautar shanu da ragunan Layya da ya aikawa jama'a a Zuru. Wanna ya auku ne sakamakon korafi da wasu jama'ar Zuru mazauna garin Birnin kebbi ke yi tare da wasu jama'a a garin Zuru.

Yombe ya ce " Kyauta ne na bayar, kuma wanda na ga dama zan ba kyauta na, ba wai dole sai na ba wani ba, ko mutum a gidana yake sai na ga dama zan ba shi. Na ba mutanen Zuru har Yauri da garin Birnin kebbi. Idan masu korafi sun dubi yatsun hannu, ai tsawon su ba daya ba. Saboda haka masu korafi za su iya isar da korafinsu a yadda suka ga dama".

ISYAKU.COM ya samo cewa Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe Dabai, ya aika da shanu da raguna fiye da talatin Zuwa Masarautar Zuru domin rabawa jama'a da ya tsara.

Wani Badakkare mazauni garin Birnin kebbi da baya son a ambaci sunansa, ya yi zargin cewa " A gaskiya ni kam ban ji dadi ba kuma ban gamsu da yadda wanda ya kamata ya zama babban wakilin jama;ar mu a jihar Kebbi ya yi biris da mutanenmu wajen bayar da kyautar ragunan Salla ba. Domin ni kam ban san mutum daya da ya sami rago daga Baba Yombe ba daga Zuru a nan garin Birnin kebbi daga kyauta da ya yi kwanan nan ".

Ya kara da cewa " Idan ma har ya bayar, kamata ya yi ya nemi shugaban jama'an Zuru mazauna garin Birnin kebbi, kuma a yada labari da hotunan yadda aka bayar da ragunan ko kyautarsa, tunda harkar siyasa ce kuma wakilcin siyasa ne. Akasin haka yana nuni da wani ra'ayi ne komabayan muradun jama'a da yake wakilta".


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN