Ke Duniya: Duba dalili da ya sa Ibrahim Magu ya koma kwana cikin Masallaci

 Legit

Wani rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa mukaddashin shugaban hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC, Ibrahim Magu, ya daina kwana cikin ofishin yan sanda kamar yadda yayi kwanaki hudu da suka shude.

Magu, wanda ke fusktantar bincike gaban kwamitin fadar shugaban kasa karkashin Alkali Ayo Isa Salami, ya koma kwana a Masallacin dake cikin hedkwatar hukumar FCID. An tattaro cewa an gyara ofishin FCID dake Zone 10, cikin birnin tarayya tun lokacin da aka tsare Magu a wajen.

Hakazalika, an tattaro cewa manya a hukumar yan sanda sun gana ranar Juma'a, 10 ga Yuli, domin tattaunawa kan lamarin Magu. Rahoton yace manyan hukumar yan sanda sun yanke shawarar watsi da shi saboda rashin hadin kansa da hukumar yan sanda lokacin da yake cin mulkinsa a EFCC.

Majiyoyi daga hukumar sun bayyana cewa lokacin yake mulki, da gayya yake nunawa manyan yan sanda yatsa kuma ya daina halarta zamansu karkashin jagorancin IGP Adamu Muhammad. Bugu da kari, an ruwaito cewa shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi ministo ci da manyan jami'an gwamnati cewa kada su sake a gansu suna masu taimakawa Magu wannan lokacin.

Mun kawo muku rahoton cewa Lauyan Ibrahim Magu, a ranar Juma'a ya bukaci kwamitin fadar shugaban kasa dake bincike kansa ta bashi beli. Ya ce akwai bukatar sakin Magu saboda yan jarida na amfani da damar tsareshi da akayi wajen wallafe-wallafen bata masa suna.

Ya kara da wasu bukatu shida daban. Magu ya ce kwamitin na kira masu shaida kansa amma ba'a bari ya gansu balle amsa laifinsa ko kin amsawa. Lauyansa, Mista Wahab Shittu, ya bayyana hakan ranar 10 ga Yul i, 2020


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari



أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN