Ibrahim Magu ya kwashe wasu komatsansa daga ofishin EFCC

Shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu ya kwashe wasu komatsansa daga shelkwatan hukumar a cewar rahotun Jaridar Tribune Online.
 
Rahotun ya ce  Magu ya umarci wasu jami'ansa su kwashe wasu daga cikin komatsansa daga ofishinsa a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa fadar shugaban kasa ranar Talata domin ci gaba da fuskantar binciken Kwamiti.
 
Rahotun ya kuma yi bayanin yadda masu taimaka masa a hukumar suka shigo shelkwatan hukumar da motoci biyu domin kwashe komatsansa kuma ana zaton za su sake dawowa ranar Laraba domin su karasa kwashe sauran komatsansa. 

Ibrahim Magu na fuskantar tuhume tuhume 22 a gaban wani Kwamiti da ke zamansa a fadar shugaban kasa.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari



أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN