An samu hargowa tare da kadawar zuciyar jama'a bayan wasu jirage biyu sun yi karo da juna a sashen sauka da tashi na kasa da kasa da ke filin jiragen sama na Murtala Mohammed a jihar Legas.
Wani jirgi A330-243 mai lamba OD-MEA mallakar kamfanin gabas ta tsakiya ya yi karo da wani jirgi 'Boeing 777' mai lamba TC-LJC mallakar kamfanin Turkish.
Wata majiya a filin jirgin ta ce jirgin daukan kaya na kamfanin Turkish ya na ajiye a lokacin da jirgin sama mallakar gabas ta tsakiya ya ci karo da shi.
"Shi jirgin kamfanin Turkish ya na ajiye a 'tarmac' lokacin da jirgin MEA ya zo ya yi karo da shi tare da karya wani bangare na jirgin.
"Jirgin MEA ya na kan titin yin 'gare' kafin tashi sama a lokacin da hatsarin ya faru," a cewarsa.
Tun misalin karfe 12:00 na rana jirgin MEA ke karbar fasinjoji, amma faruwar lamarin ya sa an sauke dukkan fasinjojin da su ka shiga jirgin, a cewar majiyar.
Wata majiya a filin tashin jirgin ta ce jirgin MEA ya na gudanar da kasuwancin jigilar fasinjoji bisa basajar fitar da bakin haure daga Najeeriya.
"Wadannan mutanr kasuwancinsu kawai su ke yi ta hanyar fakewa da kwashe bakin haure. Su na zuwa kasar nan a kalla sau uku a sati.
"Jirgin MEA da na kamfanin Turkish su na gudanar da kasuwancinsu ne kawai," a cewar majiyar.