• Labaran yau


  Halayen manyan Sakatarori 4 da ke jawo wa Gwamnatin jihar Kebbi farin jini ga al'ummanta

  Jama'an jihar Kebbi na ci gaba da tofa albarka da alhairi a yanayi na gamsuwa da amanna da halaye, mutunci, martaba da jinkai ta hanyar taimaka wa talakawan jihar Kebbi da wasu manyan ma'aikatan Gwamnatin jihar Kebbi guda hudu suka yi fice a kai.
  Abubakar Dutsin mari Sakataren din-din-dim ma'aikatan kudi jihar Kebbi

  Wannan lamari ya kara haskaka martaba da darajan Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu, wanda ya sa lamarin talakan jihar Kebbi gaba cikin sahun kyautatawa a Gwamnatance bisa manufa.

  Bincike da ake yi wa Magu ya kara nuna nagartar gwamnatin Buhari - Inji Malami

  Mujallar ISYAKU.COM ya samo cewa yanzu haka zancen wadannan mutane ne ake yi a jihar Kebbi ta fannin taimakon jama'a daga ma'aikatan Gwamnati.
  Garba Hamisu-Sakataren din-din-dim ma'aikatan watsa Labarai jihar Kebbi

  Wadannan Sakatarorin din-din-dim sun hada da.

  1. Alhaji Abubakar Muhammed Dutsin Mari - Sakataren din-din-dim ma'aikatan kudi a jihar Kebbi
  2. Alhaji Sufiyanu Garba Bena - Sakataren din-din-dim Sashen tsaro na Gwamnatin jihar Kebbi
  3. Alhaji Malami shekare - Sakataren din-din-dim na ma'aikatan Filaye da gidaje na jihar Kebbi
  4. Alhaji Garba Hamisu - Sakataren din-din-dim na ma'aikatan Labarai da al'adu na jihar Kebbi.

  Kwamandodin boko haram 47 sun fice daga kungiyar sakamakon rikicin kabilanci
  Sufiyanu Bena Sakataren din-din-dim sashen tsaro na Gwamnatin jihar Kebbi

  Sakamakon binciken mu ya nuna cewa, wadannan mutane suna da kwarjini a fuskan jama'an jihar Kebbi a bangaren aikin Gwamnati. Haka zalika, binciken ya samar cewa sun yi fice wajen taimakon jama'a daga abin da suka samu na rayuwa, da kuma taimakawa kai tsaye ta fannin aikin Gwamnati a karkashin ma'aikatar da suke aiki. Sakamakon haka, ya kara jawo wa Gwamnatin jihar Kebbi farin jini da gamsuwa daga talakawa.

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Halayen manyan Sakatarori 4 da ke jawo wa Gwamnatin jihar Kebbi farin jini ga al'ummanta Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama