Fafaroma ya ji takaicin mayar da cocin masallaci

BBC

Fafaroma Francis ya ce ya ji raɗaɗin matakin da Turkiyya ta dauka na mayar da ginin cocin Hagia Sophia da ke Istanbul masallaci - ya yi wannan maganar ne a karon farko tun bayan da Turkiyya ta dauki matakin mayar da gini mafi tsufa a tarihin duniya zuwa masallaci.
Fafaroma ya yi wannan bayanin ne lokacin da yake jagorantar adduar ranar Lahadi a dandalin Saint Peter da ke fadarsa ta Vatican.
An gina Hagia Sophia ne tun farko a matsayin cocin kimanin shekaru 1,500 baya.
An fara mayar da gini masallaci ne tun bayan mamayar da daular Usmaniyya ta yi wa yankin shekaru 1,500 da suka gabata, amma tun daga shekarun 1930 ta koma gidan tarihin da ba na wani addini ba.
Shugabannin addinin kirista sun ta sukar matakin shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, haka ma Tarayyar Turai da UNESCO ba su ji dadin matakin ba.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN