Duba yawan albashin da kowane dan sandan Najeriya ke karba bisa mukaminsa


Shafin intanet na musamman da aka bude domin rajistar masu sha’awar aikin ɗan sanda a Najeriya na 2020 ya fara aiki kuma ƴan kasar masu sha’awa na iya mika takardunsu daga yau.

Ga adireshin shafin domin mu sha’awa – www.policerecruitmegov.ng.Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce za a ɗauki kurata ne, wanda zai ba rundunar damar kara yawan ƴan sanda kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ba kasashen duniya shawara su yi domin inganta tsaro.

BBC ta ga bayanan da ke cikin shafin na rajistar masu neman zama ƴan sandan Najeriyar, inda rundunar ta ce wannan yunkuri ne da zai kawo daidaito da inganta matsayar Najeriya tsakanin ƙasashen duniya.

Abin da ya kamata ku sani kan aikin ɗan sanda

Rundunar ƴan sandan Najerice babbar hukumar da ke tabbatar da tsaro da oda a kasar. Suna da jami’ai a jihohi 36 na ƙasar da kuma Abuja babban birnin ƙasar.Sunan shugaban hukumar shi ne Babban Sufeton Ƴan Sandan Najeriya. 

Albashi

Yana da muhimmanci ku sani cewa, yayin da ake yin rajista, aikin ɗan sanda na wanda ke da kishin aikin ne kawai, kamar yadda Abimboa Opeyemi kakakin rundunar ƴan sandan na jihar Ogun ya shaida wa BBC:Ga albashin ƴan sandan Najeriya:
  • Kurtu – N46,000- N47000
  • Kofur- N52,000-N53,000
  • Sajan – N62,000-N63,000,
  • Mai anini 1 – N78,000
  • Sufeto Anini 2 – N123,000
  • ASP Mai Tauraro 1 – N132,000-N134,000
  • ASP – N139,000
  • DSP – N142,000-N143,000.

Alawus-alawus

Ban da albashi, akwai kuma wasu abubuwan da ɗan sanda ke mora a aikin nasa. Ana kuma biyan wasu alawus-alawus da ake biya domin samar da tsaro.Kakakin rundunar ya ce akan samar wa ƴan sanda muhallai a jihohin da aka tura su aiki na Najeriya, kuma a kan ba wadanda ba su sami muhallin na gwamnati ba kuɗi domin su biya kuɗin haya a wasu wuraren.Ana kuma samar wa ƴan sanda tsari ishorar lafiya. Saboda haka duk jami’in da ya kamu da rashin lafiya na iya zuwa asibiti ba tare da ya biya ko kwabo ba. 

Mukamai

Ga dukkan muƙaman ƴan sandan Najeriya:
  • Babban Sufeto Janar – Inspector General of Police
  • Mataimakin Sufeto Janar na ƴan Sanda – DIG
  • Mataimakin Sufeto Janar na ƴan Sanda – AIG
  • Kwamishinan Ƴan sanda – Commissioner of Police
  • Mataimakin Kwamishinan Ƴan sanda – DCP
  • Mataimakin Kwamishinan Ƴan sanda – ACP
  • Babban Sufritandan Ƴan Sanda CSP
  • Sufritandan Ƴan Sanda SP
  • Mataimakin Sufritandan Ƴan Sanda DSP
  • Mataimakin Sufritandan Ƴan Sanda ASP
  • Sufetan Ƴan Sanda – Inspector of Police
  • Samanja
  • Saje
  • Kofur
  • Las Kofur
  • Kurtu 
 Rahotun BBC

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN