Kisan da aka yi wa wata tsohuwa mai shekara 90 wacce wani boka da mutanen yankin suka zarga da maita ya tunzura 'yan Ghana.
Bokan ya zargi tsohuwar mai suna Akua Denteh da maita inda daga nan suka azabtar da ita na tsawon sa'o'i har ta rasa ranta.
Wani
bidiyo da ya yadu kamar wutar daji ya nuna yadda mutane suka zagaye
tsohuwar suka dinga dukanta da itatuwa a kanta tare da zane ta,yayin da
take zaune a kasa har sai da ta fita hayyacinta, sannan daga bisani ta
mutu.
Lamarin ya faru ne a Kafaba da ke yankin Salaga a ranar Alhamis din da ta wuce.
Rahotanni sun ce mutane sun dauki matar suka kai ta gidan bokan.
'Yan sanda a Kafaba sun dauki gawar matar suka kai mutuware a asibitin koyarwa na Tamale don yin gwaji.
Source: BBC
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/