Hajji dai yana daya daga cikin shika shikan addinin musulunci da duk musulmin da Allah ya bawa iko ake son ya yi a kalla sau daya a rayuwarsa. A sauran shekaru, ana iya cewa hajji na daya daga cikin taron addini da ke samun hallartar mutane da dama a duniya amma a bana lamarin ya canja.
Musulmi sun isa masallacin haramin na Makka inda suka fara gudanar da dawafin na zagaye masallacin haramin suna adduoi kamar yadda wasu faya fayen bidiyo na kasar Saudiyya suka suna.
An yi wa mahajjatan gwajin zazabi sannan an killace su na kwanaki 14 a lokacin da suka isa kasar mai tsarki a karshen makon da ta gabata. Anyi hakan ne don tantance masu dauke da cutar korona.
Kafafen watsa labarai na Saudiyya ya nuna yadda ake yi wa jakkunan mahajjata feshin maganin kashe kwayoyin cutar kuma wasu daga cikinsu an basu wani naura sun saka a hannunsu domin a rika sanin inda suke a kowanne lokaci.
Mahukunta a kasar ta Saudiyya sun zagaye dakin na Kaaba a bana inda suka ce ba za a bari mahajjata su rika shafansa ba domin dakile yaduwar cutar coronavirus. An kuma kara adadin asibitoci da asibitocin tafi da gidanka da motoccin daukan marasa lafiya a Makka domin kula da lafiyan cikin mahajjatan cikin idan bukatar hakan ta taso.
"Ba bu wata fargabar tsaro game a aikin hajjin amma an takaita adadin mahajjatan ne kawai domin dakile yaduwar annobar coronavirus," a cewar direktan tsaron alumma na Saudiyya, Khalid bin Qarar Al-Harbi. An kuma hana kafafen watsa labarai na kasashen duniya damar zuwa daukan rahotanni yayin aikin hajjin na bana a yunkurin da gwamnatin kasar ta yi na tsaurara matakan tsaro.
Source: Legit
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/