Duba abin da motsa jiki zai yi a lafiyar jikin ka

Motsa jiki shi ne duk wani aiki da ke faruwa bayan yunƙurin tsokokin jiki kamar tafiya, sassarfa, gudu, tuƙa keke, linƙaya, rawa, wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, da sauran ayyukan gida ko wurin aiki saɓanin zama ko kwanciya.

Motsa jiki akai-akai na temakawa wajen rigakafi da yaƙar cutukan da ba ƙwayoyin cuta ne ke janyo su ba, kamar ciwon zuciya, ciwon siga, kansa / daji da shanyewar ɓarin jiki.

Haka kuma, motsa jiki na temakawa wajen kiyaye hawan jini, ƙiba / teɓa, kuma yana bunƙasa lafiyar tunani, ingancin rayuwa da walwala.

Sai dai duk da ɗunbum alfanun da motsa jiki ke da shi, Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce duk mutum 1 cikin 4 a manyan mutane da kuma 3 cikin 4 na matasan da ke cikin shekarun balaga a faɗin duniya na bijire wa shawarwarin motsa jiki na aƙalla minti 30 kowace rana da hukumar lafiyar ta bayar.

Saboda haka, rashin motsa jiki ke lashe daga cikin kasafin kiwon lafiya har kaso 1 — 3 cikin ɗari a ƙasashe masu matsakaici da mafi ƙarancin tattalin arziƙi, hakan ma banda matsalolin da suka shafi lafiyar tunani da ciwukan ƙashi da tsoka.

Physio Hausa

Tsere da gudu don tsira da lafiyarka!

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post