Dalla dalla: Duba adadin kudaden da Najeriya ta kwato ta hanyar yaki da cin hanci

Lauyan koli kuma ministan shari'a na Najeriya, Abuabakar Malami, ya sanar da cewa kokarin da gwamnatin tarayya ta ke yi na yaki da cin hanci da rashawa, ya samar da kusan dala biliyan 63.5 a tsawon shekara guda.

A tsawon lokacin, Malami ya ce Ma'aikatar Shari'a wadda take karkashin jagorancinsa, ta tara wa kasar nan kimanin naira biliyan 2.1 da kuma dala miliyan dari takwas.

Ministan ya ce Ma'aikatar ta samu nasarar hakan ne a kimanin shari'o'i 80 na babbar kotun tarayya, manyan kotunan jiha da kuma Kotun Kungiyar raya tattalin arzikin Afrika ta Yamma wato ECOWAS.

Lauyan kolin wanda ya bayar da cikakken bayani dangane da dukiyar da aka tara, ya kuma sanar cewa Najeriya tana tsammanin dala miliyan dari biyu daga kasar Holland da kuma Switzerland.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, sanarwa Malami ta zo ne a ranar Talata cikin birnin Abuja yayin gabatar da nasarorin da ma'aikatarsa ta samu tun daga ranar 29 ga Mayu, 2019 zuwa ranar 28 ga Yulin 2020.

Ministan ya ce nasarorin da aka samu a lokacin daga yaki da cin hanci ya hada da $ 62b da aka kwato a matsayin kudaden haraji daga kamfanonin mai; kusan $ 1b (daga OPL 245 - Malabu); $ 311m (daga Abacha loot III) da $ 6.3m (daga Abacha loot IV).

Ministan ya ce nasarorin yaki da cin hanci da rashawa da aka samu a tsawon lokacin sun hadar da kudaden da aka kwato na dala biliyan 62 a matsayin basussukan haraji daga kamfanonin mai.

Sai kuma kimanin dala biliyan 1 daga rijiyoyin mai na OPL 245 da ke Malabu, da dala miliyan 311 na kudaden Abacha III da kuma dala miliyan 6.3 na kudaden Abacha IV.

Ya kara da cewa, kasar nan ta kuma tara Naira 685,784,757.09 daga tsarin nan na busa usur din fallasa masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati da kuma naira miliyan 500 ta hanyar gwanjon kadarorin da gwamnatin ta kwace.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN