Da duminsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da wani Sanatan arewa a gidansa

Rahotun Legit

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Taraba ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon mamba a majalisar dattijai, Sanata Zik Sunday. Sanata Sunday ya wakilci sanatoriyar Taraba ta kudu a majalisar dattijai daga shekarar 2003 zuwa 2007.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraba (PPRO), DSP David Misal, ya tabbatar da faruwar sace Sanata David ga manema labarai a Jalingo. DSP Misal ya bayyana cewa an sace Sanatan ne a gidansa da ke karamar hukuma Karim Lamido, amma ana kokarin kubutar da shi.

Kakakin rundunar 'yan sandar ya sake bayyana cewa gungun wasu 'yan bindiga sun sace babban limamin masallacin ofishin rundunar 'yan sanda, Mustapha Badamasi, jami'an dan sanda mai mukamin kofural.

Ya ce an sace Badamasi a gidansa da ke unguwar Sabongari a Jalingo, babban birnin jihar Taraba. Misal ya bawa iayalan mutanen da aka sace tabbacin cewa rundunnar 'yan sanda za ta yi iyakar bakin kokarinta wajen kubutar dasu tare da kama wadanda su ka yi garkuwa dasu.

A wani labarin mai nasaba da wannan da Legit.ng ta wallafa, 'yan bindiga sun sace babban limamin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, Mallam Mustapha Nuhu. An yi garkuwa da babban dan sandan ne a daren ranar Lahadi, 12 ga watan Yuli, kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.

 'Yan bindiga, da za su kai 10, sun tsinkayi gidan Malamin da ke kwatas din Nana Aisha a tsakar dare tare da sace shi. Malamin, kuma babban dan sanda, ya na aiki da rundunar 'yan sandan jihar Taraba. An gano cewa yayi wa'azi a kan yawaitar laifuka musamman garkuwa da mutane a jihar Taraba yayin hudubar Sallar Juma'a.

A lokacin rubuta wannan rahoton, masu garkuwa da mutanen basu tuntubi iyalan dan sandan ba. Jaridar Daily Trust ta gano cewa, 'yan bindiga na ta kai hari a tsakiyar birnin Jalingo a cikin makonnin baya bayan nan.

An gano cewa, unguwannin da abun yafi shafa sun hada da kusa da gadar Donga, Baba Yau, Mile 6, Kona, Wuro Sambe, Sabongari da yankin firamare. An gano cewa mazaunan yankin na cike da tsoro tare da fargabar masu garkuwa da mutanen


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari



أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN