Buhari ya goyi bayan ministansa bayan sabani da 'yan majalisa kan ayyuka 774,000

Rahotun Legit

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci karamain ministan kwadago, Festus Keyamo, da ya ci gaba da shirin daukar aikin da 'yan majalisar tarayya suka hana shi.

Manyan majiyoyi daga fadar shugaban kasar sun tabbatar da hakan ga jaridar The Cable. Keyamo ya yi cacar baki da majalisar dattawa a kan cewar su za su tsara yadda daukar aikin za ta kasance.

Kwamitin majalisar tarayya a kan kwadago ya dakatar da fara diban aikin sakamakon hatsaniyar da ta shiga tsakaninsu da karamin ministan.

A wani taro da suka yi a watan Yuni, mambobin kwamitin sun kusa bai wa hammata iska tsakaninsu da ministan inda daga bisani suka koreshi daga majalisar.

Amma Keyamo ya zargesu da yunkurin kwace daukar aikin tare da son amshe guraben don amfanin kansu da makusantansu. Ya kara da zargar 'yan majalisar da kokarin kalubalantar hukuncin shugaban kasar.

Ya ce 'yan majalisar sun dauki mataki da ya fi karfinsu. The Cable ta gano cewa Keyamo ya samu ganawa da shugaban kasa inda ya bayyana mishi abinda ya faru a majalisar a kan shirin.

Shugaban kasar ya matukar fusata da yadda 'yan majalisar ke son yin katsalandan a al'amarin da ya shafi masu zartarwa.

Ya bukaci ministan da ya ci gaba da shirin kuma ya tabbatar da an yi shi bisa tsarin da ya dace na shari'a. Ya kara da bukatar darakta janar na NDE da ya tsayar da duk wani tsari na daban a kan shirin wanda yake yi tare da kwamitin majalisar tarayya.

An kuma tattaro cewa, ministan shari'a, Abubakar Malami, ya rubuta wasika ga 'yan majalisar da su kiyaye iyakokinsu.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa za a bai wa gwamnonin jihohi, 'yan majalisar tarayya da ministoci gurbi na musamman a ayyuka 774,000 da gwamnatin tarayya za ta dauka.

Kwamitin zaben ma'aikatan ne ya bayyana hakan a jiya Laraba yayin sanar da yadda daukar wadanda za su ci moriyar shirin za ta kama, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Shugaban kwamitin a jihar Bauchi, Sanusi Aliyu Kunde, ya sanar da hakan yayin rantsar da kwamitin na jihar.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN