Bincike da ake yi wa Magu ya kara nuna nagartar gwamnatin Buhari - Inji Malami

Atoni janar na tarayya, Abubakar Malami, ya ce binciken Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu da ake yi ya kara nuna nagartar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Malami ya fadi hakan a wani shirin NTA a daren ranar Juma’a, da yake mayar da martani ga tambayoyin mai gudanar da shirin, Cyril Stober.
AGF din ya bayyana cewa binciken dakataccen Shugaban na EFCC ya nuna cewa babu wanda ya fi karfin doka, Jaridar The Punch ta ruwaito.
Da yake amsa tambaya kan ko ana gudanar da binciken don wani rashin jituwa da ke tsakaninsu ne, ministan shari’an ya ce ba shine ke binciken EFCC din ba, cewa fadar shugaban kasa ce ta kafa kwamitin binciken.
Malami ya ce: “kafa kwamitin da fadar shugaban kasa ta yi domin binciken ayyukan hukumar yaki da rashawa ci gaba ne.
“Ya kasance abunda aka san wannan gwamnati a kai; na rashin tsoro ko yin alfarma idan har abu ya shafi bincike a kan zargin rashawa. Don haka, Ina ganin ci gaba ne wanda aka san gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kai cewa babu wani zargin rashawa da zai tafi ba tare da an bincike shi ba. Don haka ci gaba ne ba abun kunya ba.”
Fadar shugaban kasar ta dakatar da Magu da manyan jami’an EFCC kimanin 11 ciki harda sakataren hukumar, Ola Olukoyede.
Ana zargin hukumar EFCC karkashin Magu da rashin bayar da bayani daidai kan kudaden da aka kwato daga mahamdama.
Ana kuma zargin shugaban EFCC da siyan wasu kadarori a Dubai da ya kai naira miliyan 570.
An tsare Magu na kimanin kwanaki 10 kafin aka sake shi. Sai dai ya karyata zarge-zargen da ake masa.
Duk wani yunkuri na dakataccen shugaban na EFCC domin ya kare kanshi a gaban kwamitin ya ci tura.

Source: Legit

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN