Legit
Duk da cewa hukumar DSS ta musanta rahoton cewa ta damke mukaddashin shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, na tsare a ofishin yan sanda kuma a nan ya kwana.A misalin karfe 10:15 na dare bayan kwamitin binciken fadar shugaban ta kammala yiwa Ibrahim Magu tambayoyi, jami'an yan sandan sun yi awon gaba da shi ne daga fadar shugaban kasa.
An dakatad da dogaransa kafin aka iya tafiya da shi.
The Nation ta samu labarin cewa bayan zaman tambayoyin da akayi masa, an shigar da Magu wata motar fara kirar Hilux mai lamba 37ID.
Amma Magu ya ce sam ba zai shiga ciki ba, sai dai ya zauna a bayan motar.
Daga baya yan sandan suka shawo kansa ya shiga cikin motar.
Daga karshe dai aka garzaya dashi ofishin binciken hukumar yan sanda FCID cikin motarsa.
Wata Majiya tace: "Sakamakon binciken dake gudana yanzu, ya zama wajibi a garkame Magu a FCID. Bamu son ya koma ofishinsa yayinda ake bincikensa, saboda akwai yiwuwan a cigaba da yi masa tambayoyinsa da kwamitin Ayo Salami."
An samu labari daren jiya cewa da yiwuwan a dakatad da Magu daga Ofis.
"Hanashi komawa ofishinsa alama ce dake nuna cewa za'a dakatad da shi."
"Ya bayyana karara cewa fadar shugaban kasa ta kammala shirin neman sabon wanda zai maye kujerar." Cewar Majiya.
A misalin karfe 10:50 na dare, Magu ya ki amincewa ya kwana cikin wani ofishi a FcID.
Ya cewa yan sandan su shigar da shi cikin kurkuku kawai.
Yace: "Ba zan shiga in kwana cikin wani ofishi ba, na gwammace in kwana cikin kurkuku. Kawai ku sani cikin Kurkuku. Abinda Allah ya nufeni da shi kenan. Ba zan iya kalubalantar haka ba."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari