Rundunar yansandan jihar Enugu sun kama wata mata mai shekara 24 bisa zargin azabtar da mai yi mata aikin gida yar shekara 10 mai suna Nneoma Nnadi.
Kakakin rundunar yansandan jihar Enugu Daniel Ndukwe Ikea ya ce an kama matar ce mai suna Ifeoma Ozougwu mai shekara 24 tare da mijinta mai suna Jude Ozougwu mai shekara 40 bayan matarsa ta yi amfani da dutsin guga mai zafi tare da ababen azabtarwa da dama ciki har da amfaani da kusa ta murda a kan yarinya mai yi masu aiki a gida.
Lamarin ya faru ne ranar 2 ga watan Juli a unguwar Akonameze da ke birnin Enugu.
Kwamishinan yansandan jihar CP Ahmad Abdur-Rahman ya umarci Kwamandan shiya na yansandan Enugu ya kai yarinyar Asibiti domin samun kulawan Likitoci ganin irin halin da yarinyar ta shiga sakamaon raunuka da ta samu wajen azabtarwa da aka yi mata.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Tags:
HOTO