• Labaran yau


  Amitabh Bachchan ya kamu da cutar Korona, duba abin da ya bukaci makusantarsa su yi

  Legit

  Fitaccen jarumin masana'antar Bollywood, wanda ya yi suna a duniya, Amitabh Bachchan, ya kamu da muguwar annobar nan da ta game duniya tare da zama ruwan dare.

  Jarumin mai shekaru 77 ya kamu da cutar kuma an kwantar da shi a asibiti a ranar Asabar a garinsu na Mumbai. Ya yi kira ga makusantansa da su garzaya don yin gwaji, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

  "Na kamu da cutar korona kuma an mika ni asibiti," Bachchan ya rubuta yayin da yake sanar da cewa an yi wa iyalansa da hadimansa gwaji amma suna jiran sakamako.

  "Duk wadanda suka kusanceni a kwanaki 10 da suka gabata, ina kira garesu da su garzaya don gwaji!" ya kara da cewa.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Amitabh Bachchan ya kamu da cutar Korona, duba abin da ya bukaci makusantarsa su yi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama