Allah ya yiwa na hannun daman Atiku, Adamu Modibbo rasuwa

Wani jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Adamu Modibbo, ya rasu a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuli.
Madibbo wanda ya kasa nce aminin tsohon mataimakin shugaban kasa, ya rasu yana da shekaru 63 a duniya.
Marigayi Madibbo ya taba neman takarar kujerar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP) a 2003.
Daga bisani ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) inda ya nemi tikitin jam’iyyar a 2019.
Hadiminsa, Ahmed Jauro Katuka, ya fada ma jaridar Daily Trust cewa marigayin ya rasu a asibitin kwararru a Yola.
Ya kuma bayyana cewar kafin mutuwar nasa ya yi fama da ciwon siga mai tsanani.
Moddibo ya rasu ya bar matan aure biyu da yara tara. Za a yi jana’izarsa daidai da koyarwar addinin Islama.
Marigayin wanda ya kasance lauya kuma ma’aikacin banki, ya yi aiki tare da bankin First Bank Plc kafin daga baya ya zama manajan darakta na Sigma Pension Ltd.
Ya kasance a cikin shugabannin kamfanoni da dama, ciki harda Adamawa Beverages Ltd, wadanda suke ruwan Faro.
A wani labari na daban, mun ji cewa Geoffrey Onyeama, ministan harkokin wajen Najeriya, ya kamu da cutar korona.
Onyeama ya sanar da hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuli, cewa yana kan hanyarsa ta zuwa cibiyar killacewa.
"Na yi gwajin cutar korona karo na hudu a jiya bayan alamun ciwon makogwaro, sai dai kuma abun binciki shine ya bayyana ina dauke da cutar a wannan karon.
"Wannan ita ce rayuwa, ka yi nasara a nan, ka fadi a can. Ina hanyar zuwa cibiyar killacewa kuma ina addu'ar dacewa da mafificin alkhairi," ya wallafa.
Source: Legit

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN