Yanzu yanzu: Shugaba Buhari, Gwamna Bagudu da sauran Gwamnonin APC na ganawar sirri

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na cikin ganawar sirri tare da gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a fadar Shugaban kasa da ke Abuja. Jaridar The Nation ta ruwaito cewa jam’iyyar mai mulki na fama da rikicin shugabanci a kwanakin nan.

Wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; Shugaban kungiyar gwamnonin arewa, Simon Lalong da kuma gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru.

Koda dai ba a bayyana cikakken bayani kan ganawar ba, an tattaro cewa baya rasa nasaba da matsalolin da ya kunno kai a ikin jam'iyyar mai mulki. Ganawar na zuwa ne bayan Buhari ya gana da shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, a yammacin ranar Lahadi, inda ya ce shugaban kasar zai yi kokarin ganin an sasanta rikicin.

A baya mun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya yi magana a kan rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar APC mai mulki. Lawan ya yi zancen ne bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Aso Villa.

An fara rikicin shugabancin jam'iyyar ne bayan kotun daukaka kara ta dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomhole inda ta jaddada hukuncin babban kotun tarayya. Jam'iyyar ta bayyana Abiola Ajimobi, tsohon gwamnan jihar Oyo da ya bayyana a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar tunda shine mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa.

Amma tsohon mataimakin sakataren jam'iyyar na kasa, Victor Giadom ya bayyana kansa a matsayin mukaddashin shugaban dogaro da umarnin da wata kotu ta bada a watan Maris a lokacin da aka fara dakatar da Oshiomhole. Lawan ya sanar da manema labarai cewa ba za a bar wannan al'amarin ya hargitsa APC ba don daidaituwar na daidai da daidaituwar Najeriya.

Jam'iyyar ce ke juya akalar mulkin kasar nan. Shugaban majalisar dattawan ya kalubalanci shugabannin jam'iyyar na kasa da su yi namijin kokari wurin sasanta 'ya'yanta. Ya jaddada cewa, "Da izinin Allah nan da kwanaki kadan za mu ga an dauki mataki kuma akwai fatan dukkan shugabannin jam'iyyar a fadin kasar nan za su saka baki."

Rahotun Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN