Daga cikin alamun da masu shanyewar ɓarin jiki kan fuskanta akwai matsanancin ciwon kai kafin ko yayin afkuwar shanyewar ɓarin jiki a ƙwaƙwalwa. Wani bincike ya nuna cewa kaso goma sha takwas cikin ɗari (18%) daga cikin masu shanyewar ɓarin jiki 2,506 sun fuskanci ciwon kai yayin afkuwar shanyewar ɓarin jiki.
Haka nan, ciwon ɓarin kai mai zuwa tare da matsalolin gani ko hajijiya / juwa gargaɗi ne na haɗarin afkuwar shanyewar ɓarin jiki.
Saboda haka, mai ciwon kai ya gaggauta zuwa asibiti idan matsalolin gani kamar ganin bakan gizo ko dindimi suka biyo bayan ciwon kai.
Physio Hausa
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari