Miji ya daure matarsa ya aske gashin kanta ya yi ta caka mata wuka a kai har ta mutu

Wani magidanci a unguwar Lekki da ke birnin Ikko watau Lagos, ya kashe matarsa daga bisani ya halaka kanshi da hannunsa.

Wani makwabci da baya son a ambato sunansa ya ce, "Haka kawai muka fara jin sautin rikoda mai karfi kuma hakan ya dame mu. Sai muka je muka shaida wa masu kula da wannan rukunin gidaje domin su yi wa mai inda sautin ke fitowa magana domin ya dame su.

Nan take masu gadi tare da masu gidajen suka je domin isar da sako. Sun tarar da kanwar matar tare da yara a benen kasa, suka shaida mata cewa ta je ta gaya wa yayarta ko mijin yayar cewa sautin da suka sa yana damun makwabta.

Daga nan sai ta hau bene na sama inda suke ta sami kofar dakin a rufe, ta yi ta kwankwasa kofa amma ba wanda ya amsa. Sai ta dawo ta shaida wa jama'a.

Sakamakon haka aka je aka karya kofa. Amma nan ne aka tarar cewa mijin ya daure hannayen matar kuma ya manne bakinta da soletape.  Ya yi amgani da abin aski ya aske gashin kanta, kuma ya dinga caka mata wuka kala kala a kai har ta mutu, daga karshe ya sha guba ya mutu".

Dan sanda mai bincike kan lamarin ya tabbatar da faruwar lamarin, domin tuni yan sanda suka fara bincike kan lamarin.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari