Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya kayyade wa manyan hafsoshin tsaron lokacin magance matsalar tsaro a kasar, kuma ya kore su idan suka kasa.
Ahmed Lawan ya ce rayukan ‘yan Najeriya sun fi komai muhimmanci kuma kare su shi ne babban aikin gwamnati don haka dole ne hafsoshin tsaron su yi aikinsu yadda ya kamata ko su san na yi, tun da sun gaza.
“Ba zai yiwu a yi ta tafiya haka ba, dole a kayyade lokacin magance matsalar. Yanzu matsalar tsaro musamman ta Boko Haram da ‘yan bindiga a yankin Arewa, ita ce abu mafi kamata a magance.
Ya ci gaba da cewa, “Dole su tashi su yi aikinsu ko kuma a kore su”, domin gwamnati ba ta da zabi face ta magance matsalar, sannan wajibi ne a wadata hukumomin tsaro da kayan aiki da ma’aikata domin su yi aikinsu yadda ya kamata.
“Na kuma gaya wa Shugaban a Kasa cewa shirye Majalisa take da ta amince da karamin kasafin kudi don samar da isassun kayan aiki da ma karin ma’aikata ga hukumomin tsaro domin magance matsalar.Ahmed Lawan ya bayyana hakan ne bayan yi wata ganawa da Shugaba Buhari a ranar Asabar, inda ya ce sun tattauna ne kan matsalar tsaro da ke addabar kasar da muka rikicin cikin gida a jam’iyyar APC.
Hakan na zuwa ne ‘yan kwanaki baya shi Buharin da kanshi ya ce wa hafsoshin tsaron sun gaza a aikinsu kuma ba su da uzuri.
Ya yi kalaman ne a ganawarsa da su, bayan masu zanga-zanga sun bukaci ya sauka a kujerarsa sakamakon matsalar hare-haren ‘yan bindiga da suka addabi jihar Katsina, mahaifarsa da makwabtanta na Zamfara, Sokoto da Kebbi da Kaduna.
Rahotun Jaridar Aminiya
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari