A yayin da kashe - kashen rayuka da asarar rayuka suka cigaba da faruwa a arewacin Najeriya, gamayyar kungiyoyin kishin arewacin Najeriya sun bawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wa'adin kwanaki 14 ya sauya dukkan shugabannin rundunonin tsaro.
A cikin wani jawabi da gammayyar kungiyoyin guda bakwai suka fitar, sun bayyana cewa zasu sanar da mammbobinsu su mamaye tituna a sassan arewacin Najeriya domin gudanar da babbar zanga - zanga matukar Buhari bai sauya shugabannin rundunonin tsaron ba.
Gamayyar kungiyoyin sun yi barazanar cewa za su barke da zanga - zangar da zata durkusar da harkokin gwamnati idan Buhari ya ki daukan matakin da suke bukata.
"Abin takaici ne cewa sai gamayyar kungiyoyi sun yi wa gwamnatoci tuni a kan nauyin da ke kan wuyansu na bukatar kare rayuka da dukiyoyin jama'ar da suka zabesu.
"Shugaba Buhari ya samu kuri'un 'yan arewa saboda suna son ganin sauyi, suna tunanin cewa zai kawo karshen kashe - kashen da mayakan kungiyar Boko Haram ke yi, musamman ganin cewa shi kansa shugaba Buhari tsohon soja ne," a cewar gammayyar kungiyoyin.
Jawabin gamayyar kungiyoyin ya bayyana cewa tura ta kai bango, a saboda haka sun gabatar da bukatunsu ga shugaba Buhari kamar haka;
1. "Shugaba Buhari, a matsayinsa na babban kwamandan rundunonin tsaro na kasa ya gaggauta sauya shugabannin hukumomin tsaro."
"Kazalika, mu na so a binciki tare da gurfanar da duk wasu jami'an tsaro da suke rayuwar fantamawa da jin dadi; rayuwar da ta wuce samunsu na halak."
2. "A haramtawa gwamnonin jihohi kashe makudan kudi da sunan kunshin tsaro ba tare da wani bata lokaci ba."
Kazalika, gamayyar kungiyoyin sun bayyana goyon bayansu ga tsarin samar da 'yan sandan sa kai a fadin kasa.
A cewar jawabin mai dauke da sa hannun Isa Abubakar, gamayyar kungiyoyin sun bayyana cewa ba zasu zauna suna ji, suna gani ana kashe 'yan arewa ba tare da gwamnati ta dauki wani tartibin mataki don kawo karshen lamarin ba.
Sun bayyana cewa gwamnati tana da zabin daukan mataki a cikin sati biyu masu zuwa ko kuma su fuskanci babbar zanga - zanga da zata tilastasu daukan matakin da ya dace.
Rahotun Legit
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari