Kayya: Mahaifi ya dinga dukan yaransa 2 suna barci da tabarya har suka mutu

Yansandan jihar Anambra sun kama wani mahaifi dan shekara 34 mai suna Ifeanyi Apusiobi daga garin Azu Ogbunike a karamar hukumar Oyi bayan ya kwantare diyansa biyu da tabarya har lahira.


Wannan mutum ya sami yayansa masu suna Chinecherem Apusiobi mai shekara 7 da kaninsa Obinna Apusiobi mai shekara 5 suna barci sai ya dinga dukansu da tabarya har suka mutu. 


Daga bisani kuma ya yi wa mahaifinsa mai shekara 72 manyan raunuka a kai.


Yansanda sun kai gawakin yaran Asibiti inda Likita ya tabbatar da mutuwarsu.


Yansandan sashen CID suna gudanar da binciken sirri kan lamari.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari