Ka gaji da shan maganin ciwon gwiwa kullum? duba abin da za ka yi

Daga cikin nau'o'in ciwon gwiwa da mutane ke fama da shi akwai ciwon gwiwa wanda a yaren kiwon lafiya ake cewa "amosanin gaɓar gwiwa", wato "Knee Osteoarthritis" a turance, wannan ciwo ne da har a yanzu wasu mutane ke da tunanin ciwon sanyi ne. Tabbas wannan ciwo ba shi da alaƙa da sanyi ko kaɗan.

Irin wannan ciwon gwiwa yana faruwa ne sakamakon zaizayewar gurunguntsin gaɓa wanda shi ne matashin da ke tsakanin ƙashi da ƙashi domin ƙasusuwan gwiwar su riƙa gogayya da juna ba tare da tirjiya ba.

Kasancewar gaɓar gwiwa gaɓa ce da ke ɗawainiyar dakon nauyin jiki tun daga kai har zuwa gwiwa a lokutan tsaiwa ko tafiya da kuma buƙatar motsawarta a mafi yawan lokuta yayin zirga-zirga, hakan ne ya sa ciwon ke kama gwiwowin biyu dukka duk da cewa ciwon gwiwa ɗaya na iya fin na ɗayar a lokaci guda.


Bincike ya nuna cewa wannan ciwon gwiwa na gaba-gaba a jerin larurorin da ke iya kassara ko ma durƙusar da mutane ɗungurungum. Saboda haka, tasirin ciwon yana da babbar illa ga ingancin rayuwa, walwala da tattalin arziƙin masu fama da wannan ciwo.

Alamun ciwon amosanin gwiwa

Masu irin wannan ciwon gwiwa su kan fama da:

1) Ciwo mai ɗabi’ar tsuko a cikin gwiwa, musamman da daddare ko da safe.

2) Kumburin gwiwar ƙafa.

3) Riƙewar gwiwa.

4) Idan ma ciwon ya ta'azzara akan ji sautin gugar ƙasusuwan — ƙurus-ƙurus yayin lanƙwasa da miƙar da gwiwar ko kuma yayin tafiya.

Haka nan, yau da gobe ciwon gwiwar kan haifar da canje-canje a gaɓar gwiwa kama daga ƙasusuwan, zuwa gurunguntsai, tantanai da tsokokin da ke aiki akan gwiwar. Misali, raguwar tazarar da ke tsakanin ƙasusuwan gwiwa, ɗaurewar gungun tsokokin cinya na baya, da kuma raunin gungun tsokokin cinya na gaba, da dai sauransu.

Masu haɗarin kamuwa da irin wannan ciwon gwiwa sun haɗa da:

1. waɗanda shekarunsu suka miƙa.

2. masu ƙiba.

3. masu haɗarin samun rauni ko bugu a gwiwa, musamman ga masu wasannin guje-guje da tsalle-tsalle.

4) waɗanda sana'o'insu ke buƙatar ɗaukan nauyi da daɗewa a tsaye, da dai sauransu.

Kasancewar wannan ciwo yana faruwa ne yau da gobe, kaɗan da kaɗan, kuma yana da matakan ciwo da naƙasu hawa-hawa.

Matakan ciwo ko naƙasun gwiwa:

Akwai matakin farko, mataki na biyu da mataki na uku.

1) Mataki na farko shi ne yake da mafi ƙarancin ciwo da naƙasu.

2) Mataki na biyu kuwa shi ne matsaƙaicin ciwo da naƙasu.

3) Sai mataki na uku shi ne lokacin da zaizayewar ta kai matuƙa kuma shi ne mafi tsananin ciwo da naƙasu.

Don haka, samun sauƙin wannan ciwon gwiwa yana da alaƙa da ɗaukar matakan gaggawa, tun da wuri, domin fara shawo kan matsalar ciwon. Misali, matakin farko na ciwon zai fi sauƙin magani a kan mataki na uku. Saboda haka, akwai matuƙar buƙatar garzayawa asibiti da zarar an fara jin ciwon gwiwa domin shawo kan ciwon cikin gaggawa.

Sai dai, yawancin masu fama da wannan ciwo na ɗaukar ɗabi'ar nan ta shan magunguna rage ciwo barkatai domin rage raɗaɗin ciwon gwiwar. Amma waɗannan magunguna ko kaɗan ba sa warkar da wannan ciwo, sai dai sukan iya rage raɗaɗin ciwon na wani ɗan lokaci kawai. Saboda waɗannan magunguna suna da ƙayyadajjen lokacin da suke ɗauka suna aiki a jikin mutum, idan wannan lokaci ya cika to aikinsu na rage raɗaɗin ciwo ya ƙare, don haka wannan ciwo zai dawo har sai an sake shan wani maganin kuma.

To yaushe mutum zai daina shan maganin kenan?

Tabbas babu lokacin daina shan maganin rage ciwo idan ba a je wurin ƙwararrun likitocin da ya kamata ba.

Likitocin fisiyo (Physiotherapists) ne ke lura da masu irin wannan ciwo. Waɗannan likitoci suna dubawa, sannan su yi maganin ciwon a sauƙaƙe ta hanyar amfani da na'urorin magance ciwo na zamani ba tare da shan magunguna ko dogaro da magani kullum ba.

Bayan nan, za su bayar da keɓaɓɓen atisaye na musamman na ciwon gwiwa domin tsokokin da ke aiki a kan gwiwa su sami ƙarfin iya riƙe ƙasusuwan gwiwar yadda ya kamata ba tare da suna gugar juna ba.

Sannan suna koyarda dabarun motsa jiki a cikin ayyukan yau da gobe domin kiyaye ire-iren motsin da ka iya ta'azzara ciwon.

Bugu da ƙari, sukan bayar da magunguna na musamman da za su temaka wajen dakatar da zaizayewar gurunguntsi da kuma haɓaka tsatstsafo da shi domin tabbatar da ingancin lafiyar gaɓar.

Daga ƙarshe, idan duk waɗannan hanyoyi ba su yi nasarar shawo kan wannan ciwo ba, hakan na iya tilasta ɗaukar matakin ƙarshe wajen magance ciwon, wato ɗaukan matakin yin tiyata/aiki domin yin dashen gwiwa da zai maye gurbin zaizayayyen gurunguntsin gaɓar. Ana ɗaukar matakin yin tiyata/aiki ne idan ba a je asibiti a kan lokaci ba, domin shawo kan matsalar har sai da ciwon ya kassara gaɓar gwiwar.

Idan kana fama da ciwon gwiwa, tuntuɓi likitocin fisiyo (Physiotherapists) a yau a asibiti mafi kusa da kai a sashin fisiyo kai tsaye domin duba ka.

No photo description available.

Daga Physio Hausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari



إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN