Ba masu zanga-zanga za ku kama ba, ‘Yan ta’adda za ku kama – Kungiyar Cislac ga ‘yan Sanda

Kungiyar rajin tabbatar da ayyukan majalisa masu alfanu a ƙasar nan, wacce aka fi sani da CISLAC, ta yi alawadai da kama daya daga cikin shugabannin gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya da ‘yan sanda suka yi.Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun daraktanta, Auwal Ibrahim Musa Rafsanjani

CISLAC ta ce ta kadu sosai duba da yadda ta ga an yi watsi da mutunta ‘yancin demokradiyya da na ‘yan kasa.

An kama Nastura Ashir Shariff da safiyar Laraba 17 ga watan Yuni, bayan da ya halarci wata zanga-zanga wacce kungiyarsu ta CNG ta shirya domin nuna rashin goyon baya da irin kashe-kashe da ake yi a jihar Katsina dama wasu jihohin arewacin ƙasar nan.

A cewar CISLAC, “amfani da karfin jami’an tsaro kan masu zanga-zangar lumana zai iya haifar da tashin hankali maras tushe.”

An kama Nastura ne bisa zargin cewa ya zagi mai Magana da yawun shugaban kasar Najeriya, Femi Adesina.

Tuni matasa da dama suka fara bayyana bacin ransu a kafafen sada zumunta domin kama Nastura da aka yi

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a Najeriya ita ma ta fitar da wata sanarwa kan shafin Twitter inda ta umarci hukumomin Najeriya da su sake shi cikin gaggawa.

A cewar Amnesty “Nastura bai yi wani laifi ba, kawai ya fito ne domin fafutukar kawo karshen rashin tsaro a arewacin Najeriya”.

Daga ɓangarenta kuwa, CISLAC ta jaddada yadda “hukumomi ya kamata su yi amfani da karfin da suke da shi wajen kawo karshen ta’addanci wanda ya mamaye yawancin sassan Najeriya, maimakon kama masu zanga-zangar Lumana.”

A cewar dokokin kasar Najeriya, mutane suna da ‘yancin yin zanga-zanga da fadin albarkacin bakinsu da kuma ‘yancin a mutunta su.

Bisa wadannan dokokin ne CISLAC ta yi kira da a saki Nastura da duk wadanda aka kama ba bisa doka ba cikin gaggawa.

Rahotun Jaridar Alummata

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN