An kama wani tsoho mai shekara 80 mai suna Muhammed Bara'u dan asalin Mazabar Gashua a jihar Yobe bisa zargin yin lalata da wata marainiya mai shekara 10 a Duniya.
Bayanai sun ce wannan tsoho ya yi ta jan hankalin yarinyar ta yin amfani da Cakuleti, daga karshe ranar Asabar da ta gabata ya yi nassara a kanta bayan ya bukaci ta shiga dakinshi ta dauko wani abu, sai ya bi ta a baya ya rufe daki kuma ya yi lalata da ita da karfin tuwo.
An kama wannan tsoho ne bayan Kwamitin Shari'a a karamar hukumar tare da wasu kungiyoyi masu zaman kansu NGO's sun kai koke ga mahukunta.
Binciken Asibiti da aka gudanar kan yarinyar ya tabatar cewa tsohon ya yi mata fyade, wannan yarinya ta rasa iyayenta bayan sun rasu shekara biyar da suka gabata.
Za a mika binciken lamarin zuwa sashen CID a Shelkwatar yansanda a Damaturu, babban birnin jihar Yobe ranar Juma'a 19 ga watan Yuni.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI