1. Bayan cika kyawun sifar fuska, fefan kunne na amfani ne a matsayin bututun da ke tattaro sauti zuwa cikin kunne.
2. Kunne na ɗauke da sashin 'tsarin daidaito', wato 'vestibular system'. Wannan 'tsarin daidaito' shi ne ke samar da daidaituwar gangan jiki. Misali, shi ne ke bai wa mutum damar ya tsaya a tsaye cak ba tare da ya tasgaɗe ko ya karkace ba. Haka nan, wannan tsari shi ne ke ankarar da mutum cewa ya karkace ko ya yi layi yayin da yake tsaye ko zaune. Kuma rikecewar wannan tsari na daga cikin matsalolin da ke kawo cikas wajen tafiya da kuma janyo hajijiya / juwa.
3. Dodon kunne, wato 'cochlea' a turance, shi ne ke sarrafa sauti sannan ya sauya shi zuwa saƙonnin lantarki don aikewa da su zuwa ƙwaƙwalwa domin ta bayar da fassarar sautin da mutum ya ji a kunnensa.
4. 'Dauɗar kunne' kamar yadda Bahaushe ke kiran ta, sai dai a gaskiyar
lamari 'dauɗar kunne' ba dauɗa ce da aka sani ba. A likitance, 'dauɗar
kunne' wani ruwa ne mai ɗan kauri da ɗanko da kunne ke samarwa don bai
wa cikin kunnen kariya daga baƙin abubuwa da ka iya shigowa daga waje
kamar ƙura, yayi, gashi, ƙwayoyin bakeriya da sauransu. Danna wannan
link don ganin cikakken bayani kan amfanin dauɗar kunne da illar
ƙwaƙwale ta:
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=679364076136195&id=196502401089034
5. Ƙashin da ya fi kowanne ƙashi ƙanƙanta a jikin mutum na nan a taskiyar kunne, wanda ake kiransa da 'stapes' a turance.
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari