Yanzu yanzu: Kotun Kano ta bayar da umarnin kama wani shugaban karamar hukuma

Wata Kotun Majistare ta bayar da umarnin kama shugaban karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano Kabiru Ado Panshekara.

Wannan ya biyo bayan gazawar shugaban karamar hukumar bayyana a Kotu domin ya amsa gayyata da aka yi inda ake tuhumarsa da karkatar da taimako da aka bayar domin taimaka wa jama'a sakamakon cutar Korona, amma ake zargin cewa ya karkata taimakon kuma ya ba wadanda ya ga dama.

Mai gabatar da kara Salisu Tahir ya yi zargin cewa wanda ake kara ya saba wa sashe na 315 na dokokin Penal Code da sauran sassan dokoki,

Saidai Lauya mai wakiltar wanda aka yi kara ya ce shi bai san inda wanda ake kara yake ba a halin yanzu. Ya kuma bukaci Kotu ta dakatar da umarnin na minti 30.

Daga karshe an daga shari'ar zuwa ranar 27 ga watan Mayu domin ci gaba da shari'ar.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post