Yadda yan bindiga suka sace Amarya da babban kawarta

Rahotun Legit Hausa
A kalla 'yan bindiga 50 ne suka tsinkayi garin Yankara da ke karkashin karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina a ranar Asabar da ta gabata.
'Yan bindigar sun yi awon gaba da wata amarya tare da babbar kawarta ana saura sa'o'i 48 daurin aure, SaharaReporters ta ruwaito.
Wani ganau ba jiyau ba, ya ce 'yan bindigar sun tsinkayi kauyen wurin karfe 11:30 na dare inda suka yi awon gaba da Shanu.
Ya ce sun isa kauyen a kan babura kuma da dare a lokacin da mutane da yawa suke bacci. Sun isa gidan amarya tare da bukatar a miko ta da babbar kawarta.
Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina dai yace cutar coronavirus ba matasala bace a jihar, matasalar 'yan bindiga ta sha gaban annobar.
A cikin wata daya tak da ya gabata, 'yan bindiga sun halaka a kalla mutum 100 a jihar Katsina.
A wani laari na daban, wani matashi mai suna Sadiq Abubakar Ibrahim ya tsinci kansa cikin mawuyacin hali bayan Yansandan babban birnin tarayya Abuja sun harbe shi yayin da yake yin alwala a kofar gida.
Punch ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Mayu a gidansu dake Gwarimpa yayin da Yansandan sanye da kayan gida dauke da bindigogi suka far ma gidan nasu.
Sai dai Yansandan sun ce suna bin sawun wani mai garkuwa ne a unguwar a lokacin da suka ga Abubakar ya tsere daga ganinsu, don haka suka dauka shi ne barawon, sai suka bindige shi.
Amma a bangarensa, Abubakar da Iyayensa sun bayyana cewa sun dauka Yansandan yan fashi da makami ne ko kuma masu garkuwa da mutane, don haka suka razana, kowa ya tsere.
Kwamandan Yansandan ya bayyana cewa jami’ansa sun ce masa ba su harbi Sadiq ba,yankewa yayi da wayar karfe dake kan katangar gidan makwabcinsu da yayi kokarin tsallakawa.
A cewar Fatima da kyar Yansanda suka basu Sadiq don a kai shi asibiti duk da cewa yana da zubar da jini, kuma basu sake duba shi ba, balle su biya kudin asibitinsa.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN