• Labaran yau


  Yadda wasu matasa biyu sun fada hannu bayan sun aikata wani abin kunya

  An damke wasu samari biyu bayan sun shiga wani gida suka saci Pant da rigunan nono na mata  a Kajola Ajaba a jihar Osun ranar Asabar 23 ga watan Mayu.

  Karkashin jagorancin wani matashi mai suna Friday, wanda ake yi wa inkiya da "Frayo" ya jagoranci aiwatar da satar kafin sun fada hannun kungiyar tsaro ta Amotekun na jihar Osun.

  An sami samarin da Pant na mata guda biyar, rigunan nono na mata da wani guntun gatari.

  An mika samarin ga jami'an rundunar yansanda domin gudanar da bincike.

  A kudancin Najeriya, satar Pant da rigunan nono na mata ya zama ruwan dare, lamari da ake alakanatawa da ayyukan tsafi domin neman Duniya.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda wasu matasa biyu sun fada hannu bayan sun aikata wani abin kunya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama