Taimakon Ministan shari'a Abubakar Malami ga talakawan jihar Kebbi ya jawo yan kallo

Tallafin dubu dubatan buhun shinkafa da Ministan shari'a kuma babban Atoni janar na Najeriya Abubakar Malami (SAN) na ci gaba da isa ga jama'ar jihar Kebbi wanda hakan ya kawo sauki tare da waraka a rayuwan wasu daga cikin talakawan jihar Kebbi.

Cikin kyakkyawa kuma ingantaccen tsari rabo, taimakon kayan abinci, shinkafa, man girki da sauransu na ci gaba da taba hannayen mabukata a sako da lungu na jihar Kebbi a cikin watan Ramadan.

Tsarin taimako na Minista Malami, ya sha ban ban da sauran tsarin bayar da tallafi da sauran jama'a ke yi a jihar Kebbi, domin dai a tsarin Malami, akan tabbatar cewa taimakon talaka ya isa hannunsa tare da ingattacen tsarin kididdiga lissafi.

Wata majiya ta shaida mana cewa cewa, za a ci gaba da bayar da wannan taimako har bayan watan Ramadan. A kokarin Abubbakar Malamai na ganin ya inganta rayuwar talakan jihar Kebbi ta hanyar kare mutunci da martabarsa a ko ina yake a fadin jihar.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN