Rahotun Premiumtimes Hausa

Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana cewa mafi yawan wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a jihar masu sayar da tarkacen kayan wayar selula ne.

Umahi ya yi wannan bayani a ranar Laraba, lokacin da ya ke wa manema labarai bayanan mako-mako dangane da halin da jihar ke ciki kan cutar Coronavirus.

Ya yi bayanin a Gidan Gwamnati da ke Abakaliki, babban birnin jihar, kamar yadda Kakakin Yada Labarai, Francis Nwaze ya fitar da sanarwa.

“Mutum 6 daga cikin 11 da suka kamu, duk sana’ar sayar da tarkacen kayan wayar GSM su ke yi.”
Duk da Gwamna Umahi bai bayyana sunayen su ba, ya bayyana kananan hukumomin da kowane ya fito da kuma yadda ya shiga jihar dauke da cutar da kuma jihar da ya dauko ta.

“Mutumin da aka fara samu da cutar Coronavirus a wannan jiha, dan asalin Karamar Hukumar Onicha ne, daga Jihar Ondo ya dawo dauke da ita.

“Mutum na 2 da na 3 duk ‘yan asalin Karamar Hukumar Izzi ne, kuma daga jihar Delta suka dawo dauke da cutar.

“Na 6 kuma miji da mata da dan su. Kuma abin mamaki, duk wadanda ake samu dauke da cutar, babu wanda ya nuna wata alama a jikin sa.”

Gwamna Umahi ya ce da zaran sun warware a fitar da su daga cibiyar killacewa, za jarin kama sana’ar noma domin dogaro da kai da bunkasa arziki.

Ya kuma ce ba zai tsaya bata lokaci ba wajen sake garkame mutane a gida, matsawar ya ga cutar na kara fantsama.