Azumin Ramadan: Duba hanyoyin da za ka bi ka kare kanka daga tsananin kishin ruwa

Rahotun Legit Hausa

A lokacin azumin watan Ramadan, yana da matukar muhimmanci mutum ya ci abinci mai gina jiki sannan ya sha ruwa ko ababen sha domin gusar da kishi yayin sahur da bayan bude baki. Kishin ruwa yana iya janyo mutuwar jiki, bushewar labba, kishi da ciwon kai. 

Hakan yasa ya ke da muhimmanci mutum ya rika shan ruwa da abubuwa masu dauke da ruwa a lokacin azumi. 

Duk da cewa mai azumi ba zai sha ruwa ba har sai faduwar rana, akwai wasu matakai da zai dauka domin rage kishin ruwa mai tsanani. 

1 - Guji shan ababen sha masu dauke da caffeine: Caffeine wani sinadari ne da ke cikin ganyen shayi, coffee da sauransu kuma yana sanya yawan fitsari wanda hakan ke fitar da ruwa da gishiri daga jikin dan Adam. Shan caffeine mai yawa zai sanya kishi sosai saboda haka zai fi dacewa mutum ya sha ruwa ko kuma kayan itatuwa yayin sahur da bude baki. 

2 - Ka bude baki da kayan marmari da ganyaye: Baya ga iganta lafiya da kayan itatuwa da ganyaye keyi, suna kuma taimakawa wurin magance kishi saboda jikin dan adam ya kan sarrafa su a hankali ne wanda hakan zai sa ba za aji kishi da wuri ba bayan cin kayan marmari da ganyaye.

3 - Guji yawan gishiri da yaji: Gishiri da yaji da kayan kamshi na girki suna kara sanya kishi saboda haka idan mutum zai yi girki sai da takaita gishiri, yaji da kayan kamshi. 

4 - A rika yin wanka da ruwan sanyi: Yin wanka da ruwan sanyi a lokacin watan Ramadan yana taimakawa mutum wurin rage jin kishin ruwa. Yin wankan yana rage zafin jikin mutum wanda hakan na nufin ba zai yi gumi sosai ba ya zubar da ruwan jikinsa. 

5 - Guji kwalkwalan ruwa mai yawa cikin kankanin lokaci: Shan ruwa mai yawa lokaci guda ya kan sanya mutum ya yi saurin fitsarar da ruwan saboda haka ya fi dacewa mutum ya rika shan ruwan kadan-kadan bayan an bude baki. 

6 - Takaita shiga rana ko wuri mai zafi sosai: Yana da wahala mai azumi ya kauracewa shiga rana ko wuri mai zafi baki daya amma yana kyau ayi kokarin kauracewa tsananin zafi. Zafi ya kan sanya gumi wanda hakan ke janyo kishin ruwa. Mutum ya rage yawo cikin rana ya rika zama a inuwa.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN