Yanzu yanzu: An sake samun mutun 8 da suka kamu da cutar coronavirus, sun zama 232 a Najeriya

Rahotun Legit Hausa

Rahotanni daga hukumar yaki da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC), ya nuna cewa an sake samun karin mutane takwas da suka kamu da cutar COVID-19 wacce aka fi sani da coronavirus.

A bisa ga rubutun da hukumar ta NCDC ta wallafa a shafinta na Twitter ta bayyana cewa biyar daga cikinsu suna Jahar Legas, biyu a Abuja sannan kuma daya a Kaduna. Jumullar wadanda suka kamu da cutar sun zama 232 kenan, 33 daga cikinsu sun warke, yayinda biyar suka mutu.

A gefe guda mun ji cewa Gwamnatin jihar Legas a ranar Lahadi ta sanar da cewa an sake sallamar mutane biyar masu cutar Coronavirus bayan samun waraka a asibitin jinyar cututtuka dake unguwar Yaban jihar. Gwamnan jihar Legas da kansa,

Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita da yammacin Lahadi, 5 ga watan Afrilu, 2020. Yace: "Ya ku al'ummar jihar Legas, a jiya (Asabar) na sanar muku cewa mun sallami mutum daya daga asibitin jinyar cututtuka dake Yaba.

A yau Ina farin cikin sanar muku cewa mutane biyar (maza biyu da mata uku) cikin akwai wani dan shekara 10 da haihuwa sun samu waraka daga cutar #COVID19."

 "Tuni a mayar da wadannan mutane biyar wajen iyalansu. Yanzu jimillan mutane 29 suka samu waraka tare da sallama a asibitinmu dake Yaba." "Duk da cewan akwai alamun nasara kan cutar COVID-19, ya kamata mu zange dantse wajen takaita yaduwarta."

Har ila yau mun ji cewa Gwamnatin jihar Osun ta sallami mutumin farko da ya kamu da cutar Coronavirus tare da mutane 109 da suka shiga jihar daga kasar Birtaniya da Cote d’Ivoire, bayan an tabbatar basu dauke da cutar.

Gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola, ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da manema labarai a gidan gwamnatin jihar dake Abere, Osogbo.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN