Tsohon shugaban kasa Babangida ya aika wa Buhari ta'aziyyar mutuwar Abba Kyari

Rahotun Legit Hausa

Tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida ya shiga cikin sahun wadanda su ka yi magana game da rasuwar babban hadimin shugaban Najeriya, Malam Abba Kyari. Jaridar Tribune ta rahoto Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya na yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ta’aziyyar rashin da ya yi na shugaban ma’aikatan fadarsa. Ibrahim Babangida ya fitar da jawabi ne a ranar Lahadi, 19 ga watan Afrilun 2020.

Malam Abba Kyari ya rasu ne a ranar Juma’a bayan ya yi fama da cutar COVID-19 na makonni. Babangida ya bayyana Marigayin a matsayin mutum mai kishi, da tsantseni da dabara. Tsohon shugaban ya kuma bayyana Abba Kyari da wanda ya cancanci mukamin da ya rike.

A cewarsa, Abba Kyari ya bautawa kasarsa Najeriya da gaske, kuma ya nunawa shugaba Buhari amana a matsayin abokinsa kuma mai ba shi shawara na tsawon shekara da shekaru. “Kyari ya kasance a ko yaushe shirye ya ke da ya ba ka taimakon da ka ke bukata wajen dabbaka tsare-tsare da manufofin gwamnatinka.” Janar din ya ce shugaban kasar ya yi rashi.

 “Ba ni da shakka ko kadan game da cewa Kyari ya yi duk ayyukan da aka daura masa kamar yadda ya dace, ganin yadda ya san aiki kuma ya cancanta, ya kasance mai gaskiya.” Babangida ya kuma bayyana Marigayin a matsayin mutum maras girman kai.

“A kullum ya kan sa mutanen kasar nan farko, sannan Najeriya sai kuma karon kanka a bakin aikinsa.” “Babu tababa, kai da Iyalinsa za su ku fi kowa jin rashin Abba Kyari, a matsayinmu na Musulmai mun yarda cewa za mu komawa Mahallicinmu, Allah Madaukaki mai iko kan rayuka.”

“An rahoto a wani hadisin Manzon Annabi Muhammad SAW cewa duk wanda annoba ta kashe, ya mutu shahidi, ina addu’ar ace Kyari ya dace da falala da martabar shahada.” Inji sa. Tsohon shugaban kasar ya ce Buhari ya rasa aboki, abin kauna, amini, wanda ya yi wa kasa aiki tare da hakuri da kishi a Malam Abba Kyari, wanda ya mutu a ranar mai daraja ta Juma’a.

A karshe Babangida ya yi kira ga Buhari a matsayinsa na jajirtaccen Musulmi mai imani kuma tsohon Soja, ya dage wajen ganin an yi maganin wannan annoba ta COVID-19 a Najeriya.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN